Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar FIFA Ta Siyar Da Tikiti Sama Da 742,760 Na Gasar Cikin Kofin Duniya 2018


Kungiyar kwallon kafa ta duniya FIFA, ta bayyanar da rahoton yawan tikitin shiga kallon gasar kwallon cin kofin duniya na shekarar 2018 “World Cup 2018” da za’a gudanar a kasar Rasha.

An dai siyar da tikiti 742,760, a zagayen farko na siyar da tikitin, kamun nan da ranar Juma’a da ake sa ran kulle siyar da tikitin a zagayen farko. Wasan da ake sa ran bugawa a shekara mai zuwa.

Kimanin kashi 53% na tikitin da aka siyar ‘yan kasar ta Rasha ne suka siya, sai kashi 47% kuwa an siyar da su ga mutane daga sauran kasashen duniya, masu sha’awar zuwa kallon wasan kai tsaye.

Kudin siyan tikitin ya fara da kudin Uro 79 zuwa Uro 829 dai-dai da naira N35,000 zuwa N370,000, inda ‘yan kasar zasu biya Uro 17, wajen siyan tikitin. Za’a fara siyar da tikitin a zagaye na biyu daga ranar 5 ga watan Disamba, zuwa 31 ga watan Janairu 2018.

Masoya wasan kwallon kafa daga kasashen Amurka, Brazil, Germany, China, Mexico, Israel, Argentina, Australia, da Ingila su suka kwashe kaso 10 na siyan tikitin. “Gaskiya munji dadin yadda siyar da tikitin ya kasance ya zuwa yanzu” a cewar Mr. Falk Eller, shugaban siyar da tikitin na kungiyar FIFA.

Hakan na nuna cewar masoya wasan kwallon kafa suna da yawa a ko’ina a fadin duniya, za’a siyar da tikiti milliyan 2.5 a baki daya zagaye 64, na wasannin da za’a buga a filaye 12, tsakanin jihohi 11, na kasar Rasha. Masu bukatar siyan tikitin kuwa, zasu iya siyan tikitin a shafin yanar gizo na kungiyar fifa.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG