Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Barcelona Da Manchester City Ke Kan Gaba


Sakamakon wasannin da aka buga na lig lig ranar Jumma'a 24/11/2017, Celta Vigo ta doke Leganes da ci 1-0, sai ranar asabar Alaves ta sha kashi da ci 2-1 a hannun Eibar, Real Madrid ta kwaci kanta daci 3-2 a wasan data biuga tsakaninta da Malaga, sai Real Betis ta yi kunnen 2-2 da Girona, Atletico Madrid, ta lallasa Levante da kwallaye 5-0.

A ranar lahadi 26/11/2017, Deportivo da Athletic Bilbao, sun tashi 2-2, sai Real Sociedad inda suka sulhunta 2-2 tsakaninta da Las Palmas, Villarreal 2-3 Sevilla, Valencia tayi kunnen doki 1-1 da Barcelona.

Sai kuma wasan da ya rage tsakanin Espanyol da Getafe wanda za a buga da misalin karfe tara na dare agogon Najeriya, Nijar, Kamaru da Chadi.

Barcelona ke saman teburin da maki 35, sai Valencia take biye da ita da maki 31, Atletico Madrid tana mataki na uku da maki 27.

A kasar Ingila kuma a ranar Jumma'a 24/11/2017 an fafata a wasannin mako na goma sha uku bangaren firimiya lig, inda Westham tayi kunnen doki 1-1 da Leicester City, inda Totten ham da westbromwich suka tashi 1-1, sai kuma Manchester United ta doke Brighton & Hove kwallo 1, mai banhaushi.

Crystal palace, ta doke Stoke city, 2 da 1, Newcastle United ta sha kashi a hannun Watford da kwallaye 3-0, sai Swansea City sunyi canjaras 0-0 da AFC Bournemouth, Liverpool tayi kunnen doki 1-1 tsakaninta da Chelsea,

A ranar Lahadi kuwa Southampton ta lallasa Everton da kwallaye 4-1, Sai Arsenal ta doke Burnley da ci 1-0 a gidan Burnley, Huddersfield tana da 1 Manchester City tana da 2.

Manchester City ke mataki na daya da Maki 37, sai Manchester United a mataki na biyu da maki 29, Chelsea tana mataki na uku da maki 26.

please wait

No media source currently available

0:00 0:05:17 0:00

  • 16x9 Image

    Bala Branco

    Bala Branco ma'aikacin jarida ne a Albarka Radio FM Bauchi dake tarayyan Najeriya wanda yake shirya wa Dandalin VOA labaran wasanni, Haifaffen Unguwar Nufawa ne dake birnin Bauchi. Mazaunin Bauchi a Najeriya.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG