Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Nasiru Abdullahi Kobi Ya Sake Lashe Zaben 'Yan Jarida Marubuta Labaran Wasanni A Jihar Bauchi


Alhaji Nasiru Abdullahi Kobi
Alhaji Nasiru Abdullahi Kobi

An gudanar da zaben shugabanin da zasu jagoranci kungiyar ‘yan jarida marubuta labaran wasanni a jihar Bauchi da ake kira da turanci Sport Writers Association of Nigeria, (SWAN) Bauchi Chapters.

kamar yadda kundin tsarin mulki na kungiyar ya tanadar akanyi wannan zaben ne duk bayan kowace shekaru uku,

A wannan karon ma, an gudanar da zaben lafiya, inda aka sake zaben shugaban kungiyar wanda yake kai, Alhaji Nasiru Abdullahi Kobi, na gidan talabijin mallakar jihar Bauchi (BATV) a matsayin Shugaba domin ya cigaba da shugabantar kungiyar a karo na biyu, tare da mataimakinsa Bala Usman Kurba, na gidan Rediyo mallakar jiha (BRC) sai Sakataren kungiyar Mahmud Yakubu Muhammad, da Bala Bawaji Kwankiyal a matsayin mataimakin Sakatare.

Sauran wadanda aka zaba sun hada da Umar Ahmed Rufai, a matsayin ma'ajin kungiyar da kuma Selya Yarnap, a matsayin sakatariyar kudi.

An gudanar da Zabenne a ranar Asabar 11/11/2017 a sakatariyar ‘yan jarida (NUJ) dake cikin garin Bauchi, bisa jagoranci Alhaji Isa Hassan Jarawa, a matsayin shugaban zabe da kuma Abdulrahman Salisu Garba, a matsayin sakatare tare da sauran manbobin kwamitin.

Tuni dai aka rantsar da zababbun shuwagabanin inda suka kama aiki nan take kamar yadda doka ta tanada.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

  • 16x9 Image

    Bala Branco

    Bala Branco ma'aikacin jarida ne a Albarka Radio FM Bauchi dake tarayyan Najeriya wanda yake shirya wa Dandalin VOA labaran wasanni, Haifaffen Unguwar Nufawa ne dake birnin Bauchi. Mazaunin Bauchi a Najeriya.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG