Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mujallar Forbes Ta Ayyana Mawakiya Beyonce A Matsayin Mace Da Ta Fi Kudi


Mawakiya Beyonce
Mawakiya Beyonce

Kamfanin dillanci labarai na ‘Forbes’ ya bayyana shahararriyar mawakiyar kasar Amurka Beyonce, a matsayin mawakiya data da tafi kowace mawakiya kudi a fadin duniya.

Kamfanin jaridar ya bayyana cewar, mawakiyar ta samu kudi kimanin dallar Amurka milliyan dari da biyar $105M tun daga watan Yunin shekarar 2016, zuwa Yunin wannan shekarar 2017.

Yawon tallar faifan wakokinta na 'Formation' da tayi a shekarar da ta gabata ya shigo ma ta da karin kudi da suka kai dalar Amurka milliyan dari biyu da hamsin $250M.

A sanadiyar yawon da tayi, ya kara sa ta samu kimanin dalar Amurka miliyan sittin da tara $69M. Cikin jerin mata masu kudi akwai mawaka kamar su Taylor Swift, Celine Dion da mawakiya Jennifer Lopez, sun lashe mataki na biyar a jerin mata masu kudi a duniyar waka.

Ita kuwa Dolly Parton, ta zamo ta shida, wannan wani abin mamaki ne, mawakiyar mai shekaru 71, na da kimanin kudi dalar Amurka, miliyan Talatin da bakwai $37M, wanda take da wasu zafafan wakoki guda 63, da tayi tun a lokacin kuruciyar ta.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG