Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Za'a Kaddamar Da 'Yar-tsana Ta Farko Sanye Da Hijabi


Ibtihaj Muhammad
Ibtihaj Muhammad

Wani kamfani dake yin ‘yar-tsana a kasar Amurka, ya bayyana kudurin sa na samar da ‘yar-tsana ta farko a duniya da ke sanye da hijabi. ‘Yar-tsanar ta farko da kamfanin zai fara yi, zata fito da suffar hoton musulma ba’amkiya Ibtihaj Muhammad.

Ba’amurkiya Ibtihaj, itace mace ta farko da ta wakilci kasar Amurka, a gasar wasannanin Olympics da aka gabatar a shekarar da tagabata, inda ta lashe kambu na gwana a wasan takobi ‘Fence’ a turance.

Za’a fara sayar da ‘yar-tsanar idan Allah ya kai rai nan da lokacin bazara a shekara mai zuwa. Wannan yunkurin dai yayi dai-dai da lokacin da yakamata a karrama mata, idan akayi la’akari da irin gudunmawar su a duniya.

Musamman idan aka yi duba da kokarin su a fanin wasanni, a lokacin da matashiya Ibtihaj, take nuna jin dadinta da wannan nasarar, a shafinta na twitter tace "Nayi murna da wannan karramawar, kuma abin fahariya ne gareni, ace na zama mace ta farko sanye da hijabi da aka kirkira a matsayin ‘yar-tsana"

Idan ba’a mantaba matashiyar Ibtihaj, ta zamo ba’amurkiya ta farko da ta shiga gasar zakaru lokacin wasannin motsa jiki na Rio 2016.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG