Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bayern Munich Ta Baza Komar Ta Wajan Maye Gurbin Frank Ribery


Kungiyar kwallon kafa ta Bayern Munich, dake kasar jamus, ta ce ta baza komarta wajan neman dan wasan da zai maye gurbin shahararen dan wasan tsakiyarta mai suna Franck Ribery.

Franck Ribery, mai shekaru 34 da haihuwa zai karkare kwantirakinsa ne a kungiyar ta Bayern Munich, a karshen kakar wasan bana,

Sai dai wata majiya mai karfi ta mujallar France Football, ta rubuta a shafinta inda ta ke bayyana cewa kungiyar ta Bayern Munich, a yanzu haka hankalin ta ya karkata kan dan wasan tsakiya na kungiyar kwallon kafa ta Paris Saint-Germain, na Kasar Faransa, mai suna Julian Draxler,

Kuma kungiyar ta Bayern Munich, tace ta na da kwarin Gwiwar sayo dan wasan na PSG a karshen kakar wasan bana, inda alokacin ne Franck Ribery, zai kammala yarjejeniyar sa da kungiyar ta Bayern Munich,

A farkon kakar wasan bana ne akayi ta rade radin cewar kungiyar ta Bayern Munich tana zawarcin Draxler, sai dai alokacin kungiyar ta musanta hakan.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:54 0:00

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG