Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kamfanin BMW Zai Fitar Da Sabbin Motoci Iri 12 A Shekarar 2025


Shahararren kamfanin kera motocin kasar Germany “BMW” na kara kaimi wajen fito da motoci masu amfani da wuta, nan da shekarar 2020. Wanda suke kokarin fito da sababbin kira masu launuka daban daban. Zasu fitar da sababbin tsaruruka goma sha biyu 12.

Sun sanar da hakan ne biyo bayan yunkurin su na zamanantar da motocin su, wannan wani yunkuri ne na ganin sun shiga gaban kamfanin da suka fara kirkirar mota mai amfani da caji ta kasar Amurka ‘Tesla’

Mutane da yawa na tsoron siyan mota mai amfani da caji sabo da tsada, da kuma zamansu motoci dake da wuyar gyara. Amma tun bayan fito da sabuwar motar da kamfanin Tesla su kayi ta ‘Model S’ a shekarar 2012, sai mutane suka fara sakin jiki da sabon tsarin.

Tun daga nan kamfanoni masu kera motoci, ke shiga cikin gasar samar da mota da bata amfani da mai, wanda hakan yake da matukar muhimanci ga lafiyar mutane, wajen rage yawaitar gurbatar yanayi.

A shekarar 2013 ne, dai kamfanin na BMW suka kaddamar da sabuwar motar i3 mai amfani da wuta, sunce yanzu a shirye suke su wadatar da motar a ko’ina a fadin duniya. Daga nan zuwa shekarar 2020, motoci masu amfani da wuta zasu kara yawa.

A shekarar 2025 kuwa, zasu fitar da kirar sababbin motoci 12, da babu wadda zata dinga amfani da man fetur, a cewar shugaban kamfanin Mr. Harald Krueger, a wata zantawa da yayi da manema labarai.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG