Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Apple Ya Fitar Da Sabuwar Waya Mafi Tsada Da Daukar Hankalin Jama'a A Duniya


Sabuwar wayar kamfanin Apple ta iPhone X, itace wayar da mutane suka fi ‘dokin ganin sun mallaka tun farkon wayar iPhone da aka fara kirkira. Ranar juma’ar nan mai zuwa za a fara sayar da wayar a shaguna.

Sai dai kuma ba kamar sauran wayoyin iPhone ba, iPhone X za tayi matukar wahalar mallaka. Farashin wayar zai fara ne daga $999 wadda ta zamanto iPhone mafi tsada da aka taba yi. Wayar dai na ‘dauke da kayayyakin fasaha na zamani.

Ganin yadda mutane suka fara rububin ganin cewa sun mallaki wannan waya, ya sa wasu masu fashin baki ke hasashen ba za a iya cimma burin samar da wayoyin iPhone X ga duk mutanen da su kayi oda ba, har sai an shiga sabuwar shekara.

Ranar Juma’ar da ta gabata ne Apple ya bude hanyar da mutane zasu iya sayen wayar tun kafin lokacin fitar wayar ya karaso a shafin yanar gizo, sai ga shi shafin na kiyasin zai ‘dauki har zuwa makonni shida kafin mutane su fara samun wayoyin da suka saya.

A wata sanarwa da kamfanin Apple ya fitar ta shawarci mutane da su je shagunan Apple da wuri, domin shagunan zasu bude da missalin karfe 8 na safe.

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:13 0:00

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG