Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Za'a Haramta Amfani Da Motoci Masu Amfani Da Mai A Paris Daga Shekarar 2030


Nan da ‘yan shekaru kadan, karar mashin ko motoci zasu zama abun tarihi a cikin birnin Paris. A wani sabon yunkuri da mahukunta a kasar ta Paris, su keyi na kokarin ganin an cinma, nan da shekarar 2030.

Mahukunta a kasar na ganin cewar, ana samun karuwar matsalar dumaman yanayi da karuwar hayaniya, a cikin garuruwan su idan akayi la’akari da yadda motoci ke kai kawo.

Don magance matsalar ta dumaman yanayi, sun fitar da sabon kuduri da zai samar da motoci masu aiki da hasken rana, ko caji kadai za’a dinga amfani dasu a birnin daga nan zuwa shekarar 2030.

A cewar shugaban karamar hukumar ta Paris Mr. Anne Hidalgo, idan Allah ya kai rai shekarar 2024, babu wata mota mai amfani da man gas da zata kara shiga cikin garin. A lokacin da ake sa ran gudanar da wasannin Olympics.

A cewar mataimakin shugaban karamar hukumar, sun samar da duk wasu tsare-tsare da suka kamata, a samar don ganin an rage cinkoson motoci a birnin, da rage yawaitar karan ingina, kana da kananan cututuka da motoci masu amfani da mai ko gas kan haifar.

Ya kara da cewar, mafi akasarin mutane mazauna birnin basu da motoci, amma suna da sha’awar samun daya, wanda hakan zai kara sa garin cikin rudani, idan akace kowa yana da nashi abun hawan. Yadda za’ayi maganin dumaman yanayi shine kawai a samar da motoci da basa amfani da mai.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG