Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bincike Ya Tabbatar Da Cewar, Matasa Sunfi Son Snapchat Akan Facebook


A jiya Laraba aka fitar da sakamakon wani bincike da aka gudanar, da yake nuni da cewar, mafi akasarin matasa sun fi samun nishadi a yayin amfani da shafin Snapchat, fiye da shahararren shafin Facebook.

Kashi 47% na matasa da aka zanta dasu, a yayin gudanar da wannan binciken, sun bayyana cewar sun fi kaunar shafin na snapchat, domin shi ke basu damar bayyanar da irin halin da suke ciki a kowane lokaci.

Inda su kuma, kashi 9% suka zabi shafin na facebook a matsayin shafin da su kafi so. Sai wasu kason kuma 24% suka ce sun fi son shafin Instagram fiye da duka shafufukan facbook da snapchat.

A bangare daya kuma kaso 7% sun zabi shafin Twitter a matsayin shafin da suka fi samun nishadi akai, ana damu raguwar kaso 15% akan masoya shafin na twitter daga shekarar bara zuwa yau.

A cewar jagoran binciken Mr. Piper Jaffray, ya bayyanar da cewar, ya zanta da matasa 6,100 daga jihohi 44 na kasar Amurka. Mafi akasarin matasan masu matsakaitan shekaru ne tsakanin 15-16.

Kasancewar shafin na snapchat shine shafi da mafi akasarin matasa kanyi amfani da shi yanzu, kuma shine shafi mafi hadari ga rayuwar matasan. Domin kuwa, shafin snapchat da Instagram sunfi shafar lafiyar kwakwalwar matasa.

A cewar likitoci manazarta kwakwalwar dan-adam, wasu kadan daga cikin cututukan da shafufukan yanar gizon snapchat da Instagram, kan haifar ga lafiyar matasa sune, ciwon mantuwa da dimuwa, cutar damuwa, rashin bacci, kana da cutar kadaici, da masu makusanta da su.

A cewar Shirley Cramer, shugabar hukumar RSPH, shafufukan Instagram da snapchat suna daga cikin shafufuka na farko da suke iya shafar lafiyar matasa, kasancewar shafufukan suna dauke da hotuna, wanda kowane matashi zai so yayi abun burge wani.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG