Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Har Yanzu Manchester City Ke Jan Ragama


 Manchester City
Manchester City

A kasar Spain bangaren La-Liga mako na goma sha biyu ranar Jumma'a da ta gabata Girona 1-1 Real Sociedad,

A ranar Asabar 18/11/2017, Getafe ta doke Alaves 4-1 sai Leganes 0-3 Barcelona, Sevilla 2-1 Celta Vigo, Atletico Madrid da Real Madrid sun tashi babu ci.

A ranar Lahadi Athletic Bilbao 1-1 Villarreal, Malaga 3-2 Deportivo, Espanyol 0-2 Valencia, Las Palmas ta sha kasha a hannun Levante, da kwallaye 2-0.

A yau kuma za'a buga wasa tsakanin kungiyar kwallon kafa ta Eibar da Real Betis, da misalin karfe tara na dare agogon Najeriya da kamaru,

Barcelona take Jan ragamar teburin da maki 34, sai Valencia a mataki na biyu da maki 30, Real Madrid tana mataki na uku da maki 24.

A kasar Ingila bangaren firimiya lig a nan ma an gwabza a wasannin mako na goma sha biyu inda Arsenal ta doke Tottenham da ci 2-0 sai Leicester 0-2 Manchester city, Westbromwich tasha kashi a gidanta daci 4-0 a hannun Chelsea, Crystals palace 2-2 Everton, Liverpool ta samu nasara akan Southampton, da ci 3-0 AFC Bournemouth 4-0 Huddersfield, Burnley 2- 0 Swansea, Manchester United ta lallasa Newcastle United da ci 4-1. Watford ta doke Westham, 2-0.

A yau kuma Brighton & Hove zata karbi bakuncin Stoke City da misalin karfe tara na dare agogon Najeriya, Nijar, kamaru da Chadi.

Har yanzu dai Manchester City ke rike da teburin da maki 34 sai Manchester United, da maki 26 a mataki na biyu Chelsea ta hauro mataki na uku da maki 25.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:30 0:00

  • 16x9 Image

    Bala Branco

    Bala Branco ma'aikacin jarida ne a Albarka Radio FM Bauchi dake tarayyan Najeriya wanda yake shirya wa Dandalin VOA labaran wasanni, Haifaffen Unguwar Nufawa ne dake birnin Bauchi. Mazaunin Bauchi a Najeriya.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG