Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Idan Kida Ya Canza Dole Ne Rawa Ta Canza


Ministan Wasanni, Barrister Solomon Dalung
Ministan Wasanni, Barrister Solomon Dalung

Ministan matasa da wasani na Najeriya, Barrister Solomon Dalung, yace a wannan karo ‘yan wasan kwallon kafa na Super Eagles, da zasu wakilici Najeriya a gasar cin kofin kwallon kafa na duniya zasu jene da zammar son lashe kofin.

Ministan ya fadawa taron majalisar zartarwar Najeriya cewa kida ya canza shi yasa rawar ma ya canza, domin a wannan karon inji Ministan tawagar ta Najeriya zuwa gasar cin kofin kwallon kafa na duniya zasu je gasar ne da kafar dama.

Yana mai cewa an tattauna batun nasarar da kungiyar ta Super Eagles ta samu akan kasar Argentina, a taron majalisar zartarwar wanda yace hakan ya karawa kungiyar karfin gwiwar tunkara gasar da gaske ba a matsayin ‘yan kallo ba da ake kallon kungiyar ada can.

Ministan ya jinjinawa 'yan wasan na kungiyar ta Super Eagles da masu tafiyar da gudane gudanen kungiyar akan hadi kai domin tafiyarda harkokin kungiyar domin cimma nasarar da aka sa gaba.

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:49 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG