Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Fara Gasar Tsofaffin Masu Taka Leda


Ranar Jumma'a da ta gabata aka fara fafatawa a wasannin cin kofin kwallon kafa na maigirma dogarin Gwamnan jihar Bauchi, DSP Adamu Ahmed, wanda ya saba sawa duk shekara mai taken “ADC Cup 2017 Old Timers Football”.

Wannan gasar dai na tsofaffion ‘yan wasan kwallon kafa ne masu shekaru sama da arba'in da biyar da haihuwa.

Kungiyoyin kwallon kafa 16, ne suke fafatawa a wannan gasar ta bana Wannan shene karo na uku na gasar an bude wasann bana ne tsakanin kungiyar Spartans Fc, da kuma kungiyar M A 2019 Boys wato yaran Gwamnan Jihar Bauchi,

Spartans Fc, ta doke M A Boys da ci 2-1 dan wasan gaba na Spartans, mai suna Babangida Inuwa shi ya jefa Spartans kwallayen biyu a ragar M A Boys kafin tafiya hutun rabin lokaci,

A cikin mintuna na 32 da fara wasan sai DSP Adamu Ahmed ya jefa kwallo daya a ragar Spartans, a bugun daga kai sai mai tsaron raga.

Janar Ladan mai ritaya mai tallafawa Gwamna a harkokin tsaro ne ya wakilci Barrister MA Abubakar, har ila yau wasan ya samu halartar hukumin masarautar Bauchi.

A sauran wasannin da aka buga ranar Asabar da lahadi, Ajiya Adamu FC, tayi canjaras 1-1 tsakaninta da Nasarawa United FC.

Mighty Pillars 1-1 Monaco FC sai kuma Makera United ta sha kashi a hannun Dawaki old Stars da ci 2-0, Bakari Dukku old stars, 0 Kobi Rangers 2.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG