Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Romelu Lukaku Ya Tsallake Rijiya Da Baya


Romelu Lukaku
Romelu Lukaku

Dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Manchester United Romelu Lukaku, mai shekaru 24 da haihuwa ya tsallake hukuncin da ake tsammanin hukumar kula da kwallon kafa ta kasar Ingila wato FA zata yi masa na dakatar dashi daga buga wasanni uku sakamakon tokarin da yayi wa dan wasan baya na kungiyar Brighton & Hove, mai suna Gaetan Bong.

Lamarin ya faru ne a wasan da suka yi ranar asabar cikin wasannin Firimiya lig mako na sha uku, inda Manchester ta doke Brighton daci 1-0.

Hukumar FA ta ce ta kalli faifan Bidiyon yadda lamarin ya faru don haka babu wani hukunci da zata yi wa Lukaku dangane da abun da ya afku a lamarin sai dai ta ce zata cigaba da sa ido akan dan wasan nan gaba domin ta tabbatar da irin wannan dabi'a idan halin dan wasan Lukaku ne zata gani, in yaso anan zata dauki tsatsauran mataki a kansa.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:36 0:00

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

  • 16x9 Image

    Bala Branco

    Bala Branco ma'aikacin jarida ne a Albarka Radio FM Bauchi dake tarayyan Najeriya wanda yake shirya wa Dandalin VOA labaran wasanni, Haifaffen Unguwar Nufawa ne dake birnin Bauchi. Mazaunin Bauchi a Najeriya.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG