Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotu Ta Yankewa Robinho Hukuncin Daurin Shekaru 9


Wata kotu a Milan, kasar Italy, ta yanke wa dan wasan kasar Brazil, mai suna Robinho, hukuncin shekaru tara a gidan yari bisa samun sa da laifin aikata fyade ga wata yarinya mai shekaru 22.

Kuton tace an sami Robinho ne da hannun dumu-dumu cikin wasu gungun matasa da suka sha barasa, suka yi amfani da gushewar hankali don cinma burinsu na yin lalata da yarinyar mai shekaru ashirin da biyu da haihuwa ‘yar kasar italy.

Hakan ya farune a ranar 22 ga watan Janairu, 2013 a lokacin Robinho, yana buga wasa a kungiyar kwallon kafa ta AC Milan.

Robinho, dan shekaru 33 da haihuwa dan asalin kasar Brazil, wanda ya taba buga wasa a shekara ta 2010 zuwa shekara ta 2015 a kungiyar ta AC Milan dake kasar Italy a yanzu haka dai yana buga wasa a wata kungiyar kwallon kafa ta Atletico Mineiro, dake kasar Brazil.

Sai dai lauyansa yaki amincewa da wannan tuhumar da ake ma dan wasan inda yace maganar bata da makama, ballanta hujja.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG