Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sabon Fim Din Bollywood Mai Take 'Bayi' Akan Labarin Gaskiya


Yawaitar shiryawa da fitar da fina-finai da kungiyar shirya fina-finai ta kasar India ‘Bollywood’ keyi na dai-dai da yadda mutane ke kaikomo a cikin daji da lunguna-lunguna, don yin bayan gida. Hasalima, mutane kanyi bayan gida a kowane sararri suka samu kansu.

A ‘yan kwanakin nan ne kungiyar ta bollywood suka fitar da wani sabon fim mai suna ‘Toilet’ a turance, ‘Bayi’ biyo bayan ganin yadda mutane suka dauki zagayawa cikin daji ko lungu su biya bukatun su, abun sha'awa.

Batare da maida hankali da irin cutar da hakan ke haifarwa ga lafiya a’ummah ba, shahararren dan wasannan Akshay Kumar, shine ya fito a fim din, wanda labarin da aka bayyanar a fim din, labarin gaskiya ne.

Inda ake so a nuna matukar muhimanci, amfani da bayi, don biyan bukata, labarin dai na wata matace da ta rabu da mijinta bayan auren su, a sanadiyar babu bayi a gidan da ya ajiye ta, sai dai su dinga zagayawa bayan gari wajen biyan bukata.

Ita kuwa baza ta iya wannan rayuwar ba, sai tanemi da su rabu, alkalumman kididdiga sun tabbatar da cewar, akwai kimanin mutane sama da billiyan biyu da milliyan dari shida, a fadin duniya da basu amfani da bayi.

A kasar Indian mutane sama da billiyan daya da milliyan dari uku, basa amfani da bayi, wajen zagayawa. Wannan fim din zai yi matukar tasiri ga rayuwar milliyoyin mutane, bakawai a kasar India ba, harma da duniya baki daya.

Firaministan kasar Narendra Modi, ya dau alwashin gina bayi sama da milliyoyi a baki daya kasar, don kawo karshen wannan matsalar. Bisa ga al’adar kasar, mai tsawon tarihi, bayi abun kyama ne, domin kuwa baya bada lafiya ga dan’adam.

Suna da al’adar cewar babu yadda za’ayi a gida ace akwai bayi, kuma akwai kicin, wannan babbar kazantace a irin tasu al’adar. hakan yasa kowa sai dai ya zagaya bayan gari idan akwai bukatar hakan.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG