Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ta Gantsara Masa Cizo A Al'aurarsa


Wani mutune mai suna Miguel Francisco, ya shiga hannun hukuma a kasar Mexico, inda ake zarginsa da yin fyade, wanda ya faru a Saltillo, a jihar Coahuila, Arewa maso tsakiyar Mexico.

Kamar yadda jaridar Daily star, ta ruwaito shi da Miguel, ya tilasawa wata yarinya mai shekaru goma sha bakwai ne yin lalata da ita inda ya bukaci ta sa alkalaminsa abakinta.

Alokacin gudanar da wannan bukata tashi sai matashiyar ta gantsara masa cizo inda tayiwa alkalaminsa lahani wanda daga bisani ya kai asibiti kuma jami’an asibiti suka yi zargin cewa akwai lauje cikin nadi suka sanar da jami’an ‘yan Sanda.

Da ‘yan Sanda suka hallara a asibitin sai suka tabbatar cewa akwai abinda ya faru da mace da bisani aka gano matashiyar wanda yanzu haka a bisa doka tana da kariya na rashin abatar sunanta har tsawon rayuwartar kuma tana taimakawa ‘yan Sanda da binciken su.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG