Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dan Kungiyar Asiri Ya Kashe Sojan Najeriya


An kashe wani Soja a Ubeta, dake karamar hukumar Ahaoda ta kudu a cikin jihar Rivers, inda yanzu haka rahotani ke nuni da cewa al’umar wannan yanki na cikin fargaba da zamar zullumi.

Ana kuma zaton cewa daya daga cikin ‘yan kungiyar asirin da aka fatattaka daga karamar hukumar Ogba-Egbema a jihar ta Rivers, ne ya aikatawa wannna Sojan aika aikan.

Daga bisani Sojojin sun dauke gawar dau uwansu, sarkin garin Chimezie Nathaniel, ya bukaci mazauna garin da su kwatar da hankalinsu har sai an kammala bincike.

Koda yake a halin yanzu jama’ar garin na zaman dar dar domin gudun martini daga Sojojin da aka kashe masu abokin aiki har yanzu babu wani jawabi daga Sojojin dangane da wannan kisan.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG