Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hada Hadar Zaratan 'Yan Wasan Kwallon Kafa Na Duniya


A cigaba da hada hadar ‘yan wasan kwallon kafa na duniya da akeyi.kungiyar kwallon kafar Barcelona tace tana da tabbacin cewar ‘yan wasa, irinsu Lionel Messi, mai shekaru 30 da takwararsa Andres Ineista, mai shekaru 33 zasu sake rattaba hannun a kungiyar kafin karewar kwangilarsu a shekara mai zuwa.

Barcelona ta kuma ce zata sake sabon shiri wajan sayen dan wasan Liverpool Philippe Coutinho, kafin ranar da za'a a fitar da jaddawalin gasar zakarun nahiyar Turai,domin taga alamar Liverpool bata da niyar sayar mata da dan wasan,

Tottenham, tana yunkurin shan gaba Manchester United, wajan sayen dan wasan baya na gefen dama daga kungiyar Paris Saint German, mai suna Serge Aurier, mai shekara 24 da haihuwa akan kudi fam miliyan £23,

Ita kuwa Paris Saint German tana daf da sayen matashin dan wasannan na Monaco, dan kasar Faransa, Kylian MBappe mai shekara 18 da haihuwa,

Manchester United, tace zatayi iya kokarinta wajan ganin ta sayo matashin dan wasa baya na gefen hagu mai shekara 17 da haihuwa, Ryan, daga kungiyar Fulham,

Arsenal, tace ba wata tattaunawar da zatayi da dan wasan tsakiyarta Alex Oxlade Chamberlain, a wannan satin,

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:38 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG