Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

James Bond 007, Zai Dawo Da Sabon Salo "Bond 25"


Fim din James Bond, zai dawo da wani sabon salo, Daniel Craig, ya bayyana dawowarsa a matsayin James Bond. Jarumin ya tabbatar da dawowarsa a matsayin mai leken asirin kasar Birtaniya “Bond 25” Wanda yake sa ran sake sabunta kwangilar sa.

Ya bayyana haka ne, a yayin ganawar da wani dan jarida Stephen Colbert jiya, koda yake bayanin na shi ya baiwa mutane mamaki, domin kuwa a shekarar 2015, ya bayyana a wani shirin kasar Ingila "Time Out", cewar ya gwammace yankar naman jikin shi, da ya sake zama Jarumi a matsayin James Bond.

Ya kuma ce wannan shawar bata da madogara, yanzu haka ya kosa ya koma don fara sabon fim din na James Bond, tun bayan rattaba hannun da yayi na kwangilar shirya fim din a shekarar 2006, ya samu kanshi a cikin wata sabuwar rayuwa.

Ana kuma sa ran sabon fim din James Bond 007, mai take “Bond 25” zai fito a watan Nuwamba na shekarar 2019, idan Allah ya kai rai.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG