Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Baya Ga Harkar Barkwanci Akwai Wata Sana'ar


Mu'azu Muhammad
Mu'azu Muhammad

Wani matashi mai sanar barkwanci mai suna Mu’azu Muhammad, yace baya ga harkar barkwanci yana sana’ar sayar da amfani gona.

Mu’azu Muhammad, wanda aka fi sani da Bushkiddo, yace duk da yake cewar harkar barkwanci na kawo wuta, inji taba wata sana’ar ma akan wannan na da mahimmanci.

Bushkiddo ya bayyana haka ne a yayin da yake ganawa da wakiliyar DandalinVOA Baraka Bashir a Kano.

Ya ce ya fara harkar barkwanci ne bayan kammala karatunsa na jami'a, ya kuma ce ya faro ne tun suna makaranta kasancewa duk inda ya zauna sai ya bada dariya.

Mu'azu ya ce babban matsala da ke ciwa harkar barkwanci tuwo a kwarya mussamam ma nasu na ‘yan mintuna da ke zagawa a wayoyin salula suna fuskantar rashin bada hadin kai wajen dauka barkwancin nasu a faifain bidiyo a wurare da dama.

Ya ce baya ga harkar kasuwanci sana'ar tasa ta samawa matasa da dama aikin yi, inda ya ce ya sanya mafi yawan abokansa a harkar.

please wait

No media source currently available

0:00 0:06:16 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG