Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ya Zama Wajibi Mata Su Tashi Tsaye Domin Neman Na Kai


Sana'ar Dogaro Da Kai
Sana'ar Dogaro Da Kai

Da babu gara babu dadi kuma ance dan guntun gatarinka yafi sari ka bani sana’ar dogargo da kai abun alfaharin kowane Bil – Adam ne.

Malama Hauwa Dorayi wata mai sana’ar hajja wace kuma takan hadawa mutane kayan lefe dama na asobi na bikin idan bukatar haka ta samu ce ta furtya haka a zantawarsu da wakiliyar Dandalinvoa Baraka Bashir.

Ta ce ta shafe shekaru 7 tana wannan sana’a inda ta ce hakan na kawar mata da kananan bukatu na yau da kullum duk da cewar a yanzu ta fara zuwa wani kamfanin domin koyon aiki saboda abinda ka je ya zo a rayuwa.

Tana mai cewa babban abin da ke ci wa sana’ata tuwo a kwaryar shine yadda wasu masu sayan kayana bashi ke biyan kudaden gutsul gutsul.

Ta kuma kara da cewa ya zama wajibi mata su tashi tsaye domin neman nasu na kansu , duba da irin halin kuncin da matsin rayuwa da ake fama da shi a yanzu.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:12 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG