Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sassan Jikinta Kawai Yake Bukata


Wani dan kungiyar asiri mai suna Ifeanyi Dike wanda ‘yan sintirin yankin Eliozu dake Fatakwal cikin jihar Rivers, suka damkawa ‘yan Sanda ya gudu.

Shi dai wannan matashi ana zarginsa ne da laifin yiwa wata yarinya ‘yan shekaru takwas fyade wanda kuma daga bisani ya kashe ta domin amfani da wasu sassan jikinta.

Sassan sun hada da idanuwanta, yatsunta, al'auranta da kuma harshenta, rundunar ‘yan Sandan jihar ta tabbatar da afkuwar lamarin ta kuma dukufa wajan farautar Dike, domin gurfanar dashi a gaban shara’a.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG