Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Aikin Malanta Ingantatciyar Sana'a Ce


Maryam Abbas
Maryam Abbas

Wata matashiya Maryam Abbas, wace take ta zamar son neman ilimi tace ta nemi gurbin karantar aikin likitanci sau biyu a jami’a amma bata samu nasarar haka ba a maimakon likitanci sai aka bata gurbin koyon Physics.

Ta ce sai da ta shafe shekaru biyu ta na nema , a duk neman da tayi sau biyu bata samu damar gurbin karantar likitanci ba, duk kuwa da ta samu nasara a jarabbawan Jamb din da tayi.

Kasancewar bata maida hankali ba har ta kai ta da rashin samun nasara a wasu kwasa-kwasai amma a yanzu da ta maida hankali sai ta lura ma ashe shima kwas din na da muhimmanci duba da akwai karancin mata masu karantar wannan kwas din.

Ta ce shima ilimi ne na kimiya tunda ya na da alaka da lissafi da amfani da kwakwalwa sosai, kuma babban fatar da nikeyi shine in samu fita da sakamako mai kyau domin babban burinta shine ta zama malamar makaranta a fannin da ta karanta.

Ta kara da cewa duk ta kukan da Malamai keyi na rashin albashi ba zai karya mata gwiwa ba domin aikin koyarwa shine abinda take sha’awa

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:26 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG