Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dubun Wani Mabaraci Ta Cika


Mabaraci
Mabaraci

Wani matashi mai suna Abdullahi Abbas, wanda ya shahara wajan barace barace , ta inda yake zama makahon karya ya kamu da gamon sa.

Shi dai wannan matashi mai shekaru talatin da bakwai (37), yana amfani da wani yaro ne mai shekaru goma sha biyu (12), a matsayin dan jagora.

Dubun matashi ta cika ne a lokacin da wata mata Balkis Adeoye, wace ta kasance ma zauniyar unguwar ta Ikorodu ce ta yi masa tabayoyin wanda daga bisani ya jawo iyar tambaya.

Da ake masa tambayoyi Abdullahi Abbas, ya ce yana cikin wata kungiyar mutane ne da suka shahara wajan iya kitsa duk wata irin nakasar da zai jawo tausayi daga jama’a domin samon sadaka.

Ya kara da cewa yak an samu Naira dubu biyar da dari biyar (5,500) zuwa Naira dubu takwas (8,000), a kullum kwanar duniya, taimakon kungiyar sintirin yanke na Ikorodu ne ya ceci ransa, kuma tuni aka damka shi ga ‘yan Sanda.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG