Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Barcelona Zata Yi Tayin Karshe Kan Dan Wasan Liverpool


Barcelona, ta ce zata yi tayin karshe na fam miliyan £135, kan sayen dan wasan Liverpool dan kasar Brazil, Philippe Coutinho, Liverpool, dai a baya ta yi watsi da tayin da Barcelona, ta yi har sau uku kan dan wasan.

Kungiyar Chelsea, ta bayyana sunan tsohon mai horas da Borussia Dortmund, Thomas Tuchael, a matsayin wanda zai maye gurbin Antonio Conte, da zaran ya bar kulob din.

Chelsea, kuma tana gab da sayen dan wasan tsakiya na Leicester city, dan kasar Ingila, Danny Drinkwater, akan kudi fam miliyan £30.

Tare da dan wasan tsakiya na Inter Milan, Antonio Candreva, dan shekaru 30 da haihuwa akan kudi fam miliyan £25.

PSG ta ce zata rika biyan dan wasan gaba na Monaco, Kylian MBappe, fam miliyan £13, a duk shekara a matsayin albashi, fiye da yadda Real Madrid, za ta biya shi.

Barcelona, ta sake tayi na biyu kan cinikin dan wasan gaba na Borussia Dortmund, Ousmane Dembele, na fam miliyan £130 a baya dai Barcelona ta taya dan wasanne a kan kudi fam miliyan £90 ita kuwa Dortmund, taki amincewa,

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:47 0:00

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

  • 16x9 Image

    Bala Branco

    Bala Branco ma'aikacin jarida ne a Albarka Radio FM Bauchi dake tarayyan Najeriya wanda yake shirya wa Dandalin VOA labaran wasanni, Haifaffen Unguwar Nufawa ne dake birnin Bauchi. Mazaunin Bauchi a Najeriya.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG