Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Sintiri Sun Kama Wani Ya Saci Tukunyar Miya


Wasu ‘yan sintiri dake gadi a cibiyar horas da ayyukan albarkatun man Fetur dake jihar Delta sun kama wani matashi mai shekaru 24 da haihuwa da zargin satar tukunyar miya.

An kama matashin wanda aka bayyana sunansa a Oghenero, ne da abokansa yayin da suke cikin shan miyar.

Mujallar Daily Trust ta bayyana cewa irin wannan lamarin ya auku sau tari a wurare da dama, inda ake dandanta lamarin da yanayin tattalin arzikin da Najeriya ke ciki wanda ya yi sanadiyyar kafa kungiyar sintiri ta farin kaya domin dakile yawan satar abinci a fadin jihar.

Mujallar ta wallafa cewa a satin da ya gabata ne jami’an ‘yan sandan jihar suka kama wasu gungun matasa da suka addabi jama’ar da basu jiba basu gani ba a Warri da fashi da makami, dubun su ta cika ne yayin da suka fada hannun jami’an.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG