Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Ceto Yara Ukku Daga Hannun Masu Satar Mutane


Jami’an hukumar tsaron kasa watau Civil defence, sun ceto wasu yara ukkumaza biyu da mace daya masu shekaru tsakanin goma zuwa goma sha daya daga hannun masu satar mutane da tsafef tsafe a jihar Abia.

Su dai wadannan yara an ceto sune a yakin Aba da Obingwa dake jihar Abia, sakamakon wani rahoton da jami’an tsaron suka samu daga wasu ‘yan kasa na garin.

Kakakin hukumar na jihar ta Abia, Uchenwa Oliver, yace wadanda ake tuhumar sukan yi shigar burtu tafkar baban bola, a inda ake zubar da shara duk lokacin da suka yi niyyar aikata muguwar aniyarsu.

Sukan fakaici yara idan suka zo zubar da shara, daga nan idan suka kama kama su sais u dauresu a wani kangon gini suna jiran masu siya su kawo kudi.

Kwamandan jihar Walter Akubiri Chika, ya shawarcin jama’a masamman iyaye dasu sa ido sosai a kan ‘ya’yansu, saboda gudun fadawa hannun miyagun mutane.

XS
SM
MD
LG