Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasu Matasa Zasu Kwashe Watani Shida A gidan Yari


barayi
barayi

Wata kotun majistare dake zama a Ado Ekiti, ta daure wasu matasa biyu Adelabu Adetunji, mai shekaru talatin da shida da Abiola Ayodeji, mai shekaru ashirin da shida, har na tsawon watani shida.

Su dai wadannan matasa an samesu da laifin sata ne kamar yadda ‘yar Sanda mai gabatar da kara Monica Ikebuilo, ta fadawa kotun.

Ta kara da cewa masu laifin sunn asabtar da wata mai suna Omolulu Ogunlade, wace suka yenketa a wuya, suka kuma rabata da Naira 80,000.

A cewar mai gabatar da karar laifin ya sabawa sashe na 355, 390, sakin layi 16, na kundin laifuffukan jihar Ekiti, na shekarar 2012.

Da take gabatar da hukuncinta mai shara’a, Omolola Akosile, tace mai gabatar da kara ta gabatar da shedun da kotu ta kamsu dasu saboda haka ta yanke masu samn watini shida a gidan yari batare da sabin tara ba.

XS
SM
MD
LG