Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wani Soja Ya Sha Kashi A Kan Satar Waya


Wani mutum sanye da kayan soji wanda ba’a bayyana sunansa ba, ya tsallake rijiya da baya daga hannun wasu jama’a bayan an yi zarginsa da sacewa wata yarinya wayar hannu.

Mujallar Daily Post ta wallafa cewa yarainyar ta daga murya a wani wurin cefane da ake kira Robson Shoping Plaza, kan hanyar Okumagba Avenue cikin Warri, bayan ta gane shi.

Yayin da yayi zargin jama’a zasu far masa, sojan wanda yake sanye da kayan sarki da wuke a hannunsa yayi yunkurin tserewa daga wurin, duk da haka jama’ar sun tasar masa inda suka yi masa kofar rago kusa da wata makarantar firamare suka shigi dukansa.

Da taimakon jami’an ‘yan sanda dake gadi a rukunin shagunan, suka taimaka wajan kwace sojan daga hannun jama’ar, jami’an sun raka sojan wanda rigarsa ta ciki ta yi jina jina gidan tsohon soja Manjo Janar mai ritaya dake kusa domin tabbatar da ko soja ne da gaske.

Sojojin dake gadin gidan tsohon jami’in suka amshe shi bayan sun tarwatsa jama’ar da suka yi cin cirindo, kana wata motar soji ta dauke shi zuwa barikin sojin dake kusa, mujarllar ta wallafa cewa wasu majiyoyi daga barikin sojin sun bayyana cewa jami’an sun ki bayyana ko wanene sojin domin a cewarsu sun tura shi asibiti inda ake jiyyarsa.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG