Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wani Mahaifi Ya Kule 'Yar Shekaru 10 Kwanaki 3 Babu Abinci


Wasu mata da yara a Mugadishu suke karbar abinci da aka dafa.
Wasu mata da yara a Mugadishu suke karbar abinci da aka dafa.

Rundunar ‘yan Sandan jihar Oyo, ta ceto wata yarinya mai shekaru goma da haihuwa daga ukubar mahaifinta., a unguwaqr Ajeigbe, a garin Ibadan.

Kakakin ‘yan Sandan jihar Oyo, S P. Adekunle Ajisebutu, ya shedawa manema labara cewa ita dai wanna yarinyar ana zargin mahaifinta ne da kuleta a daki har na tsawon kwanaki ukku, ne batare da bata abinci ba.

Wani makwabcin mahaifinta ne ya kaiwa ‘yan Sanda, rahoto daga samun rahoton ‘yan Sandan ba suye kasa a guiwa ba suka nufin gidan inda suka tara da cewa mukule ukku ne mahifin nata yayi amfani dasu wajan kule dakin, wanda daga bisani suka balla.

Yace yanzu haka ana kula da yarinyar yadda ya kamata kuma an kai asibitin ‘yan Sanda, domin duba lafiyarta, amma shi kuwa mahaifin nata aka dukufa nemansa ruwa a jallo.

XS
SM
MD
LG