Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kadiri Ikhana Ya Dawo Kano Pillars


Tambarin Kano Pillars
Tambarin Kano Pillars

Hukumar gudanarwa ta kungiyar Kano Pillars ta nada tsohon mai horar da ‘yan wasan na Kano pillars, a can baya Kadiri Ikhana, a matsayin tsabon mai horar da ‘yan wasan kungiyar da Kano Pillars.

Wannan ya biyo bayan barin kungiyar da mai horar da ‘yan wasan Muhammad Babaganaru, yayi a kakar kwallon da ta gabata.

Kakakin kungiyar ta Kano Pillars, Idris Malikawa, yace ana sa ran cewa Ikhana, zai yi amfani da kwarewarsa domin lashe kofin lig, din Najeriya, a gobe talata ne za'a gabatar da shi.

A shekarar 2008, Kadiri Ikhana,ya jagoranci kungiyar ta Kano Pillars, inda ta lashe kofin Najeriya, kafin yanzu dai Ikhana, shine mai horar da kungiyar Shooting Stars na garin Ibadan.

Kungiyar ta Kano Pillars, a kakar kwallon da ta gabata it ace ta zo ta bakwai.

XS
SM
MD
LG