Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kokari Na In Kirkiro Wani Sabon Abu Ga Al'umma Ta - Inji Mukhtar Ado


Muktar Adam
Muktar Adam

Muktar Ado matashi ne da yayi amfani da basirarsa wajen kera mota mai amfani da hasken rana, a kokarinsa na fito da wani sabon abu a cikin al'ummarsa.

Ya ce sai da ya shafe shekaru biyu yana hada kayayyakin da zai kera motar kafin Allah ya bashi sa’ar hadawa.

Motar dai an hada ta da karfe, batir guda hudu mai 36 voltage sai solar panel wato farantin dauko hasken rana sai tayoyi da wasu sauran kayayyaki.

Ya ce yayi amfani da basirarsa domin kuwa har da rediyo a jikin motar, inda ya ce yana da burin bunkasa fasahar tasa domin ya inganta abinda ya fara.

Muktar ya ce iya nisan zangon karatunsa dai a sakandire ya tsaya kuma yana da burin cigaba da karatu, inda ya ce a halin yanzu matsi na rayuwa ne ya dakatar da karatun nasa.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:24 0:00

XS
SM
MD
LG