Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Babban Kalubalen Shine Yadda Jama'a Ke Yi Wa 'Yan Fim Kallon Banza -Inji Jamila Nagudu


Babban kalubalen da muke fuskanta dai bai wuce yadda ake yiwa 'yan fim kalon banza ba, kuma mutane marasa da'a inji Jamila Umar Turaki wacce aka fi sani da Jamila Nagudu.

Jarumar ta bayyana haka ne a yayin da take zantawa da wakiliyar Dandalinvoa a Kanon Nijeriya

Jarumar ta ce babban burinta dai bai wuce ta zamu furodusa ba, da zarar kuwa tayi aure toh lailai zata daina fitowa a matsayinta na jaruma, a cewarta zata daina fito wa a fage, sai dai a bayan fage, domin hakan shi ne ra'ayinta

Ta ce da zarar an dora mata camerar daukar hoto, a wannan lokaci tana manatawa da kanta a matsayinta na Jamila Nagudu zuwa abinda darakta ya umarce ta da shi.

Ta ce a sanin ta bata da wata matsala da sana'ar da take yi sai dai ga alummar gari, kuma tana da yakininin ta isar da sako da burinta na shiga wannan sana'a.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:25 0:00

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG