Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kamfanin Facebook Sun Kirkiri Dakin Baje Kolin Basira"Hardware Lab"


Shugaban Kamfanin Facebook Mark Zuckerberg
Shugaban Kamfanin Facebook Mark Zuckerberg

Shahararren kamfanin zumunta na facebook, sun kafa tarihi a fagen duniyar yanar gizo, kamfanin shine kamfanin da ya kafa tarihi a wannan zamnin, na karni na ashirin da daya. Wanda ya hada duniya waje daya. Domin kuwa mutane a fadin duniya, kan iya ganawa da wasu a sassan duniya, ko dai ta hanyar rubutu ko ta kafar aika hotunan bidiyo, da daukar su kai tsaye.

Babban shelkwatan kamfanin dake garin Silicon Valley, a jihar California ta Amurka, ya zama matattarar duk wani abu da ya shafi yanar gizo, wanda hakan shine babban burin shugaban kamfanin Mark Zuckerberg, wanda yake da burin samarma matasa aiki ba lallai sai idan matasa sunje aiki don kirkirar wani abu ba, kamar wayoyin hannu da wasu abubuwa makamanta su.

Babban burin shi shine, ya samu matasa da suke da basira, da kuma amfani da ita wajen amfannar da ‘yan uwan su matasa a fadin duniya. Shi yasa yanzu suka kirkiri wannan dakin wanda ake kira “Hardware Lab” a turance, wanda matasa zasu dinga amfani da basirar su, wajen kirkiran abubuwa masu amfani a fadin duniya.

Suna kokarin suga sun yi rawar gani fiye da wanda kamfanin Google su kayi, wanda suka kirkiri mota mai tafiya da kanta, batare da matuki ba, don haka suke nasu kokarin wajen ganin sun hada duniya waje daya, ta hanyar samar da wasu dubaru.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG