Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasu Manyan Manhajojin Sakon Gaggawa Basu Da Sirri!


Shafufukan Facebook-WhatsApp
Shafufukan Facebook-WhatsApp

Kungiyar kare hakkin dan adam ta kasa da kasa “Amnesty International” ta gabatar da wani bincike a kan wasu manhaojin aika sakon gaggawa, da zummar gano ingancin su, wajen ajiye sakon mutane da boye wasu bayanan su. Sakamakon binciken su ya tabbatar da cewar da yawa daga cikin wadannan manhajojin basu kare sirrin mutane.

Hukumar ta binciki manhajoji goma sha daya 11, inda ta samu banbance banbance masu yawa, a tsakanin yadda suke gudanar da ayyukan su. A binciken da suka gudanar, wanda ya bayyanar da manhajar sakon gaggawa na shafin zumuntar, facebook da ta Wazob, sune nagartattun manhajoji da suke da karfin kare bayanan sirri na mutun.

A cikin jerin manhajoji baki daya da akanyi amfani da su a fadin duniya, facebook da whatsapp sune suka samu kimanin maki saba’in da uku 73% cikin dari 100, da ya tabbatar da cewar suna bama kowa hakkin shi na boye bayanan sirri.

A cewar mai magana da yawun hukumar Sherif Elsayed-Ali, manhajar Whatsapp, suna amfani da wani tsari da baya bama wani damar ganin abun da wani ke tattaunawa da wani, batare da mutumin ya nuna mawani ba, kuma suna bama mutun damar zaban irin kariya da yake bukata, a shafin nashi don kada mutun yayi abu cikin duhu, gaskiya sunyi abun da ya kamata sosai.

Su kuwa manhajojin Skype, da Snapchat, basu da wadannan tsare-tsaren, don haka mutane idan suna amfani da su, sai su san da cewar basu da sirri irin yadda ya kamata ace suna da. Basa amfani da tsarin boyon sirrin mutane, wani kan iya ganin abun da wasu ke tattaunawa.

Amma sun bayyanar da irin nasu kariyar, da suke bama masu amfani da manhajojin su, na cewar a duk lokacin da gwamnati ko wata hukuma ta bukaci a basu bayanan mutun, sai sun sanar da shi kamin su bada.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG