Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Buri Na In Nemi Ilimin Zamani -Inji Sadiya Haladu


Matashiya Sadiya Haladu ta bukaci 'yan uwanta mata mussamam wadanda ke karkara da su jajirce wajen neman ilimin zamani domin magance matsalolin rayuwa.

Sadiya Haladu dai, matashiya ce da ta kaura zuwa birni daga kauyen Kura, da niyyar neman aiki domin ta taimakawa iyayenta da wasu kananan bukatu.

Ta ce shai’awa ce ta sa ta zo birni neman nata na kanta, bayan da ta fuskanci wata kawarta da ke aiki a birni ta fita wayewa da sanya kaya masu kyau.

Ta kara da cewar kaura ne ba tare da son mahaifinta ba, ta zo birnin Kano, ta kuma kara da cewa mahaifin nata ya so ta samu karatun boko, bayan da ta fita daga firamare ta zo birni.

Sadiya ta ce a yanzu dai ta samu wayewa, amma ta rasa ilimi, kuma burinta ko da bayan ta yi aure ta nemi ilimi a dakinta.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:08 0:00

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG