Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Manu Garba Ya Zama Sabon Mai Horar Da 'Yan Wasan Gombe United


Manu Garba
Manu Garba

A hada hadar ‘yan wasan kwallon kafa na duniya, kungiyar kwallon kafa ta Gombe United, dake jihar Gombe, a tarayyar Najeriya, ta nada Manu Garba a matsayin mai horar da kungiyar, Gombe United, dai ta samu haurowa zuwa gasar firimiya na Nigeria a bana.

Ita kuwa Kungiyar kwallon kafa ta El-kanemi dake Maiduguri, a jihar Borno ta kara tsawon kwantaregin mai horar da kungiyar Ladan Bosso na tsawon shekaru ukku masu zuwa.

Yayinda ita kuma kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars, ta nada Kadiri Ikhana a matsayin mai horar da kungiyar ta Kano pillars, inda ya maye gurbin tsohon mai horar da ‘yan wasan Baba Ganaru wanda ya ajeye aikin a karshen kakar wasan kwallon kafa na bana, Kadiri zai ja ragamar kungiyar na tsawon shekara daya ne.

Haka itama Kungiyar Wikki Tourist, dake garin Bauchi ta dauki Baba Ganaru a matsayin mai horar da kungiyar na tsawon shekara daya wanda ya maye gurbin Abdullahi Maikaba da ya koma Ikwa united a makonnin baya.

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:04 0:00

  • 16x9 Image

    Bala Branco

    Bala Branco ma'aikacin jarida ne a Albarka Radio FM Bauchi dake tarayyan Najeriya wanda yake shirya wa Dandalin VOA labaran wasanni, Haifaffen Unguwar Nufawa ne dake birnin Bauchi. Mazaunin Bauchi a Najeriya.

XS
SM
MD
LG