Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dan Wasan Boxing "Mike Towell" Ya Mutu, Biyo Bayan Kashi Da Ya Sha!


Dan wasan Boxing Mike Towell
Dan wasan Boxing Mike Towell
A kowane irin wasa ko sana’a, akwai abun da ake kira kaddara ko tsautsayi. Tsautsayi da karar kwanaki sun kai ga shahararren dan wasan “Boxing” dan kasar Scotland a yankin kasashen turai. Dan wasan boksin Mike Towell, ya rasu ne bayan garzayawa asibiti da akayi da shi, biyo bayan wasan da suka gwabza da abokin karawar shi. Dan wasan mai shekaru ashirin da biyar da haihuwa, a zagaye na biyar dan wasan ya jikkata, lokacin da suke karawa da dan wasa Dale Evans. Mai dakin dan wasan ta bayyanar da cewar, mijin nata ya mutu cikin sauki, da kwanciyar hankali, haka kuma duk dangin shi suna kusa da shi a dai-dai lokacin da rai yayi halin shi. Ta kara da cewar, dama dai duk cikin ‘yan kwanakin nan, yayi ta fama da wani matsanancin ciwon kai, wanda yayi jinya na kwanaki da dama. Amma wannan wasan nashi, shine ya zama sanadiyyar mutuwan shi, suna mishi fatar ya huta.
  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG