Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mai Horar Da 'Yan Wasan Najeriya Ya Makale A Jamus


Gernot Rohr
Gernot Rohr

Daga dukkan alamu, shirye shiryen da Najeriya, keyi na wasanta da kasar Zambia, ranar 9, ga watan nan da muke ciki neman gurbi a gasar cin kofin kwallon kafa na duniya, na samun cikas.

Mai horar da ‘yan wasan Gernot Rohr, dan kaasar Jamus, ya makale a kasar ta jamus bayan da hukumar kwallon kafa ta Najeriya, watau NFF, bata aika masa da tikitin jirgi ba.

Rahotani na cewa hukumar ta ce mai horar da ‘yan wasan dama wasu ‘yan wasan Najeriya, masu bugawa kungiyoyin wasan kwallon kafa a wasu kasashen da ya kamata suna Abuja, suma hukumar da bukace su dasu sewa kansu tikitin jirgin inda sun isa Najeriya, za’a maida masu kudadensu.

Tun farko dai ‘yan wasan na fushin domin tikitin yaku bayi aka ce su siyakuma suna korafin cewa tikitin farko da suka sayi domin zuwa buga wasan su da kasar Tanzania har yanzu ba’a biyar su ba

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:07 0:00

XS
SM
MD
LG