Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Cafke Wani Matashi Makiyayi Da Bindiga Mai Sarrafa Kanta A Jihra Enugu


A yayin da ake ta kokarin shawo kan matsalolin dake ta faruwa tsakanin makiyaya da talakawa a fadin Najeriya, kwatsam sai aka damke wani Bafillace matashi dauke da bindiga kirar AK47, mai sarrafa kanta a jihar Enugun Najeriya.

Wannan lamari dai ya faru ne bayan kwanaki hudu ake zargin Fulani sun kai wani mummunan hari akan alummar Attaku dake yankin karamar hukumar Nkannu, ta jihar Enugu.

Mujallar Daily Post ta wallafa cewa an kama matashin dan shekaru ashirin da haihuwa wanda ya bayyana sunansa Ibrahim Adamumale a kauyen Affa, dake karamar humkumar Udi, dake jihar ta Enugu, wata majiya ta bayyana cewa an kama matashinne da bindigar mai sarrafa kanta da harsasai ashirin da hudu.

Mai Magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Enugu SP Ebere Amaraizu, wanda ya tabbatar da afkuwar lamarin, ya ce “matashin ya bayyana cewa shi dan asalain jihar Nasarawa ne amma yana zama ne a Hausa quarters dake 9thn mile, kuma shi makiyayi ne yana da shanun da yake kiwo”.

Ya kara da cewa an kama matshinne a kokarin hadin gwiwar jami’an ‘yan sanda da kuma jama’ar kauyen, Ibrahim Adamumale ya yi kokarin harbi a iska har sau shidda kafin jami’an suka sami nasarar damke shi.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG