Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Janye Dokar Ta Baci A Talata Mafara Jihar Zamfara


Rundunar tsaron’yan sandan jihar Zamfara ta dage dokar ta baci da tasa a karamar hukumar Talatar Mafara wanda ta sa biyo bayan tashin hankalin da ya yi sanadiyyar hallaka mutance takwas.

Sanarwar ta fito ne ranar asabar daga mai Magana da yawun rundunar jami’an ‘yan sandan jihar (PPRO), dsp Shehu Muhammad a garin Gusau.

Jami’in ya bayyana cewa iyaye su kasance masu tabbatar da ganin ‘ya’yansu sun kiyaye da kumka bin doka da oda, ya kuma yi gargadin cewa duk wanda aka kama da da yunkurin tada zaune tsaye zai fuskanci fushin hukuma.

Rikicin wanda ya yi sanadiyyar rayukan mutane takwas ya samo asali ne a sakamakon zargin batanci ga addinin Islama da wani dalibi ya yi wa abokin gardamar sa a makarantar kimiyya da fasaha Abdu Gusau Polytechnic dake Talata Mafara.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG