Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Jihar Kano Zata Dauki Mataki Kan Masu Buga Kwallo A Lokacin Ayyukan Tsabtace Muhalli


Ranar Asabar data gabata gwamnatin jihar Kano ta ce zata zartar da hukumci akan duk wanda aka kama ya karya dokar tsabatace muhalli da ake yi a kowane wata a jihar.

Kwamishinan muhalli Alhaji Ali Makoda, ne ya bayyana haka jim kadan bayan kammala ayyukan tsabatce muhalli a cikin babban birnin jihar.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya ya bayyana cewa za’a kara sabon hukuncin da za’a yankewa duk wanda aka kama da laifin karya dokar da hukuncin da aka kafa da farko wanda ya hada da cin tarar kudi, da sauransu. A misali an ci gidan biredin Eaman dake kan hanyar Guda Abdullahi tarar kudi Naira dubu sittin a sakamakon gudanar da ayyukan sa a guri mara tsabta.

Haka kuma an gayyaci jami’an tashar kundila zuwa ma’aikatar kula da muhalli ta jihar Kano domin su je su bayyana dalilan da suka ake bude tashar a lokacin da ake gudanar da ayyukan tsaftace muhallin.

Mujallar Daily Post ta wallafa cewa shugaban ya bayyana cewa gwamnati zata dauki tsattsauran mataki akan iyayen da suka bar ‘ya’yan su masu buga kwallo akan hanya a lokacin da ake gudanar da ayyukan tsabtace muhalli.

Ya ce, gwamnati bazata ci gaba da sawa jama’a ido suna karya doka ba.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG