Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Sanda Sun Cafke Wani Mai Garguwa Da Mutane Domin Kudin Fansa


.
.

Rundunar ‘Yan Sanda a jihar Abia, ta ce ta cafke wani mutun da ake zargin cewa mai satar mutane ne domin kudin fansa mai suna Kingsley Sunday, shi dai wannan mutumin an cafke shine a yankin Aba, dake jihar ta Abia.

Wanda ake zargin an ce dan wata kungiyar masu satar mutane ne da tayi kaurin suna wanda aka kashe shugabanta Agbayi, wanda kuma ake kira Onye Army, a wani dauki ba dadi da jami’an ‘yan Sanda, a watan yuni na wannan shekaran.

Kwamishinan ‘yan Sandan jihar, Adeleye Oyebade, wanda ya tabbatar da hakan ga manema labarai ya ce wani dan arziki ne ya tsegunta masu sai jami’ai, suka bazama aiki suka cafke shi, amma sauran abokan tu’annatin sa sun ranta ana kare.

XS
SM
MD
LG