Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan-Wasan Kwaikwayo Da Su kafi Albashi A Duniyar Fina-Finai!


Akto Dwayne Johnson
Akto Dwayne Johnson

Kamfanin jaridar “Forbes” na kasar Amurka ya bayyanar da ‘yan fina-finai da su kafi samun kudi a sana’ar fim a fadin duniya. Shahararren dan wasan kokuwar “Wrestling” kuma mai wasan kwaikwayo na “Hollywood” Dwayne Johnson, shine dan wasa da yafi kowane dan wasa samun albashi, wanda yake samun sama da dallar Amurka milliya sittin da hudu da dugo biyar $64.5M. Dai-dai da naira billiyan goma sha tara.

Mafi akasarin kudin shi daga fina-finan da yake yi ne, kana da wasan barkwanci da ya kanyi, sai tallace-tallace da ya kanyi ma kanmfanoni. Na biyu kuwa shine dan kasar Hong Kong Jackie Chan, wanda yayi suna a duniya wajen fada da ban dariya.

Shi kuwa Jackie Chan, yana daukar kimanin dallar Amurka milliyan sittin da daya $61M, dai-dai da naira billiyan goma sha takwas, a shekara. Na uku kuwa shine akto dan kasar Amurka, Matt Damon, wanda yake samun sama da dallar Amurka milliyan hamsin da biyar $55M, wanda tayi dai-dai da naira billiyan goma sha shida.

Shima Mr. Tom Cruise, ya shiga cikin jerin sahu, wanda yake samun dallar Amurka milliyan arba’in da takwas $48M, itama tayi dai-dai da naira billiyan goma sha hudu. Daga nan sai ‘yan wasan fina-finai na kasar India “Bollywood” Shah Rukh Khan, yazo na takwas wanda yake samun kimanin dalar Amurka milliyan talatin da uku $33M, sai Kumar Akshay, yana samun dallar Amurka milliyan talatin da daya $31M.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG