Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mai Kamfanin facebook Mark Zuckerberg, Ya Sauka Birnin Legas


Wanda ya kafa kamfanin facebook Mark Zuckerberg ya ce yana farin ciki da fara koyon yanayin wata al’umma a karo na farko daga Najeriya. Zuckerberg ya isa jihar Legas ne a jiya talata a ziyararsa ta farko a kasashen dake Afirka dake yamma da hamada.

Mai kanfanin facebook ya yi wannan bayani ne a shafin sa na facebook a yayin da ya kai ziyara a wani dandali dake yankin Yaba, ta jihar Legas.

Zuckerberg ya rubuta cewa wannan shine karo na farko da ya ziyarci wata kasa dake yamma da hamada a nahiyar Afirka, ya kuma kara da cewa zai gana da masana, da ‘yan kasuwa, sa’annan kuma a yayin da yake cigaba da fahimtar yanayin al’ummar Najeriya.

Matashin ya ziyarci dandali na farko inda ya gana da yara da wasu ‘yan kasuwa wadanda suka halarci dandalin domin kirkirar manhaja da kuma baje koli.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG