Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mawakiya "Beyonce" Ta Lashe Kyauttutuka 8, Da Zama Gwarzuwa!


Mawakiya Beyonce
Mawakiya Beyonce

Shahararriyar mawakiyar kasar Amurka “Beyonce” ta tabbata cikakkiyar mawakiyar zamani. Mawakiyar dai ta, tabbata da hakan ne a lokacin da ta lashe kyautar “MTV Video Award” wannan kyautar ta mayar da ita a sahun gaba, wanda ta doke mawaka kamar su Rihanna, da Britney Spears.

Beyonce, ta lashe kyauttutuka guda takwas, wanda suka hada da kyautar bidiyo da yafi kyau na shekarar 2016, da wakoki biyar da suka fito daga cikin albom din da tayi ma suna “Lemonade” haka tayi waka kai tsaye a bayyanar jama’a.

Mawakiyar tayi jawabi, jim kadan bayan sanar da ita da aka yi, a matsayin mawakiya da ta lashe wadannan kyaututukan. Inda ta fara da mika godiya ga ‘yar ta da mijin ta, sai ta fara da masoyan ta. Baya ga haka ta bayyanar da wannan a wani matsayin cigaba da ta samu a rayuwar ta.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG