Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Pep Gaurdiola Kwararren Mai Horar Da ‘Yan Wasa Ne


Dan wasan tsakiya na kasar Spain Juan Mata, mai taka leda a kungiyar kwallon kafa ta Manchester United, ya bayana rashin jindadinsa bisa abinda ya faru a wasan Manchester United, da Leicester, inda dan wasan ya shiga cikin minti sittin da fara wasa kafi kammala wasan aka sake canjin sa.

Sai dai mai horar da ‘yan kungiyar kwallon kafa ta Manchester United, Jose Mourinho, ya bayyana rashin tsawon dan wasan ganin cewa daga baya wasa ya koma na sama.

Yayin wannan wasa Manchester United ta sami nasara akan Leicester da ci biyu da daya wanda hakan ya basu damar daukar kofin “Community Sheild” sai dai masana kwallon kafa na ganin cewa Jose Mourinho, ya aiyana sunan Juan Mata, tun farkon zuwan sa a dan wasan da zai sayarda shi.

Shi kuwa tsohon dan wasan kwallon kafa na Barcelona Xavi, ya bayyana mai horar da ‘yan wasa kwallon kafar Manchester City, Pep Guardiola, a matsayin wanda zai kawo canji a kakar wasan kwallon kafa na firimiya lig, na kasar Ingila a bana.

Xavi, ya nuna cewa Pep Gaurdiola, kwararren mai horar da ‘yan wasa ne kuma zai iya kawo canji a bisa duk kasar da yaje yakan canja wasanin na kasashen.

  • 16x9 Image

    Bala Branco

    Bala Branco ma'aikacin jarida ne a Albarka Radio FM Bauchi dake tarayyan Najeriya wanda yake shirya wa Dandalin VOA labaran wasanni, Haifaffen Unguwar Nufawa ne dake birnin Bauchi. Mazaunin Bauchi a Najeriya.

XS
SM
MD
LG