Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hada-hadar Kasuwanci Da Zawarcin Zaratan 'Yan Wasan Kwallon Kafa Na Duniya


Kungiyar kwallon kafa ta Arsenal na shirin dawo da tsohon kaftin dinta wanda yanzu haka yake taka leda a Barcelona mai suna Thomas Vermaelen wanda ya bar arsenal a shekarar 2014.

Chelsea kuma ta kammala sayen dan wasan Aston Villa mai suna Idrissa Gueye, akan kudi fan miliyan £7.1 na tsawon shekaru 4.

Barcelona na zawarcin dan wasan kasar Brazil Gabriel Jesus, itama Man City na neman dan wasan akan kudi fan miliyan £32.

Inter Milan na neman dan wasan Borussia Dortmund Aubameyang.

Daga karshe Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid dake kasar Spain tace zata bada ‘yan wasan ta har guda 2 Marco Liorente da Mariano Diaz, da kuma karin kudi fan miliyan £25 ga kungiyar Newcastle United, domin sayen dan wasanta mai suna Moussa Sissoko.

Shikuwa kuwa mikel Obi, Na Nigeria yace baya da niyar barin kungiyarsa na chelsea a wannan lokacin.

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:13 0:00
Direct link

  • 16x9 Image

    Bala Branco

    Bala Branco ma'aikacin jarida ne a Albarka Radio FM Bauchi dake tarayyan Najeriya wanda yake shirya wa Dandalin VOA labaran wasanni, Haifaffen Unguwar Nufawa ne dake birnin Bauchi. Mazaunin Bauchi a Najeriya.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG