Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Victor Moses Ne Na Bakwai A Gasar Ingila


Victor Moses
Victor Moses

Mai horar da ‘yan wasan kwallon kafar Manchester United, Jose Mourinho, yayi kira ga ‘yan wasan Manchester United dasu dauki wasan da zasu yi yau da mahimmanci domin karrama kaftin dinsu Wayne Rooney,

Manchester United zata fafata da kungiyar kwallon kafa ta Everton a matsayin karrama kaftin dinsu wanda yayi shekaru goma sha biyu ya murza leda a kungiyar kwallon kafa ta Manchester.

Shi kuwa dan wasan Super Eagle na Najeriya mai taka leda a kungiyar kwallon kafa na Westham United, Victor Moses, shine na bakwai a cikin masu zafin nama a gasar firimiya na kasar Ingila, na shekarar na shekara 2015 zuwa 2016.

An kiyasta cewa Victor Moses, ya kanyi gudun kilomita 35, a ciki sa’a guda.

Shi kuwa mai horar da ‘yan wasan kungiyar Chelsea, Antonio Conte, cewa yayi zai dawo da dan wasan tsakiya Eden Hazard, a matsyin dan wasan gaba.

A ci gaba da wasan sada zumunci da ake yi kungiya kwallon kafa ta Bayern Munich, zasu fafata da Real Madrid, AC Milan zata kara da Chelsea.

XS
SM
MD
LG